Jump to content

Kiev

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kiev
Київ (uk)
Flag of Kyiv (en) Coat of arms of Kyiv (en)
Flag of Kyiv (en) Fassara Coat of arms of Kyiv (en) Fassara


Take Yak tebe ne liubyty, Kyieve mii! (en) Fassara

Inkiya Мати міст Руських, Новий Єрусалим, Місто, де все починається da Мать городов русских
Suna saboda Kyi (en) Fassara
Wuri
Map
 50°27′00″N 30°31′25″E / 50.45°N 30.5236°E / 50.45; 30.5236
Territory claimed by (en) Fassara Reichskommissariat Ukraine (en) Fassara, Ukrainian Soviet Socialist Republic (en) Fassara, Armed Forces of South Russia (en) Fassara, Second Polish Republic (en) Fassara da Rasha
Ƴantacciyar ƙasaUkraniya
Babban birnin
Ukraniya (1991–)
Yawan mutane
Faɗi 2,952,301 (2022)
• Yawan mutane 3,481.49 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Harshan Ukraniya
Labarin ƙasa
Yawan fili 848 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Dnieper (en) Fassara
Altitude (en) Fassara 179 m
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Wanda ya samar Kyi (en) Fassara, Shchek (en) Fassara, Khoryv (en) Fassara da Lybid (en) Fassara
Ƙirƙira 482
Muhimman sha'ani
Siege of Kyiv (en) Fassara (968)
Siege of Kyiv (en) Fassara (1036)
Capture of Kyiv (en) Fassara (1203)
Siege of Kyiv (en) Fassara (898)
Siege of Kyiv (en) Fassara (1240)
Siege of Kyiv (en) Fassara (1658)
Destruction of Kyiv (1482) (en) Fassara (1482)
Sack of Kyiv (en) Fassara
Battle of Kiev (en) Fassara (1941)
Battle of Kyiv (en) Fassara
Patron saint (en) Fassara Archangel Michael (en) Fassara
Tsarin Siyasa
Gangar majalisa Kyiv City Council (en) Fassara
• Gwamna Vitali Klitschko (en) Fassara (25 Mayu 2014)
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 01000–06999
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho 44
Lamba ta ISO 3166-2 UA-30
KOATUU ID (en) Fassara 8000000000
Wasu abun

Yanar gizo kyivcity.gov.ua
Facebook: kyivcity.gov.ua Twitter: Kyiv Instagram: kyivcityofficial Telegram: KyivCityOfficial Youtube: UCfbLP1IZ4MFZqtjrUWCKVLA Edit the value on Wikidata
Tutar birnin Kyiv.

Kyiv (lafazi : /kyiiv/ ko /kyiif/) birni ne, da ke a ƙasar Ukraniya, shi ne babban birnin ƙasar ta Ukraniya kuma birni mafi girma. Tana nan a yankin arewa ta tsakiyar Yukren kusa da Kogin Dnieper. Ya zuwa watan Junairun 2022, Birnin Kyiv na da yawan jama'a 2,952,301,[1] inda ya sa birnin ya zamo birni na bakwai a yawan mutane da Europe.[2] Kyiv gari ne mai muhimmanci na masana'antu, kimiyya, ilimi, kuma cibiyar al'adu a tsakiyar Turai. Gidane ga muhimman masan'antun fasaha, cibiyoyi karatu na gaba da sakandare, da kuma yankunan tarihi.

An sanar cewa birnin ya samo asali ne daga kalmar Kyi, daya daga cikin fitattun shahidanta guda hudu wanda suka kirkireta. A yayin tarihinta, Kyiv, daya daga cikin birane mafi tsufa a Gabashin Turai, ta fuskanci jerin daukaka da kuma rudani. Watakila birnin ya wanzu a matsayin cibiyar kasuwanci a farko-farkon karni na 5, Garin mutanen Slavic a tsakanin babban hanyar kasuwanci a tsakanin Scandinavia da Constantinople, Kyiv a da ta hada hanyar ruwa da Khazars,[3] har zuwa kameta daga mutanen Varanjiya a tsakiyar karni na 9. A karkashin mulkin Varangian, birnin ta zamo babban birnin Kievan Rus', kasar Slavic ta tsakiya ta farko. An rusa ta gabaki daya a yayin kai hare-haren Mungoliya a 1240, birnin ta rasa mafi yawan ikonta a karnuka masu zuwa. Inda ta ksance a karkashin Lithuania, daga nan sai Poland, sannan kuma Rasha, birnin ta zo ta bunkasa daga cibiyar kasuwanci zuwa muhimmin cibiyar koyarwa na Tauhidi a karni na goma sha shida, sannan kuma daga baya zuwa muhimmin masana'antu, kasuwanci, da kuma gudanarwa a karni na goma sha tara.

Birnin ta kuma daukka a zamanin juyin juya hali na masana'anta na Daular Rasha a karshen karni na 19. A cikin shekarar 1918, Jamhuriyyar Jama'ar Yukren sun sanar da 'yanci daga kasar Rasha bayan juyin juya hali na Oktoba a nan kuma Kyiv ta zamo babban birni. Daga karshen yakin Sobiet na Yukre da Sobiyet na Poland a 1921, Kyiv ta kasance birnin Ukrainian SSR, kuma ta samar da babban birnin ta a 1934. Birnin ta fuskanci rushe-rushe mai yawa a yayin Yaƙin Duniya na II, amma ta farfado cikin sauri bayan 'yan shekaru daga gama yakin inda ta zamo birni na uku a girma na Tarayyar Sobiyet.

Bayan rushewar Sobiyet da kuma 'yancin Yukren a 1991, Kyiv ta zamo babban birnin Yukren, kuma 'yan asalin kabilar Yukren masu hijira sun shige ta daga sassa daban-daban na kasar.[4] A yayin sauyinta zuwa cibiyar kasuwanci da kuma zabe na dimukradiyya, Kyiv ta cigaba da kasancewa birni mafi girma kuma mafi arziki a Yukkren.

  1. "Number of present population of Ukraine 1 January 2022" (PDF) (in Harshen Yukuren). UkrStat.gov.ua. 1 January 2022. Archived (PDF) from the original on 10 August 2022. Retrieved 20 February 2023.
  2. "City Mayors: The 500 largest European cities (1 to 100)". www.citymayors.com. Archived from the original on 2 January 2010. Retrieved 19 February 2017.
  3. "Kiev". TheFreeDictionary.com. Archived from the original on 5 August 2018. Retrieved 4 July 2015.
  4. Magocsi, Paul Robert (2010). A History of Ukraine: The Land and Its Peoples (2nd, Revised ed.). University of Toronto Press. p. 481. ISBN 978-1-4426-9879-6. Archived from the original on 14 June 2020. Retrieved 9 September 2017.