Nono
![]() | |
---|---|
organ type (en) ![]() ![]() ![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
mammary gland (en) ![]() ![]() ![]() ![]() |
Bangare na |
thorax (en) ![]() ![]() ![]() |
Amfani | Shayarwa |
Arterial supply (en) ![]() |
internal thoracic artery (en) ![]() |
Venous drainage (en) ![]() |
internal thoracic vein (en) ![]() |
Sexually homologous with (en) ![]() |
male breast (en) ![]() |
NCI Thesaurus ID (en) ![]() | C12971 |

Nono yana ɗaya daga cikin manyan mashahurai guda biyu waɗanda ke kan babban yankin huhu na ƙwanƙolin firamare. Duka mata da maza suna tasowa nono daga kyallen mahaifa iri ɗaya.
Nonon mata yana dauke dawani sinadari da ake kira mammary gland, wanda aikinsa shine samar da ɓoye madararon nono domin shayarwa.[1]
Nonuwan mace halitta ce wadda ta ƙunshi churin tsoka(muscler tissue), kitse (fats), kananan bututu (ducts) da jijiyoyin jini (veins). Sai dai kitse da jijiyoyi sunfi yawa a cikin sa. Wannan ne ma ya sanya cewa girman nonon mace da laushin sa ya danganta ne da yawan kitsen da yake cikin sa, shi yasa zaku ga wata mace tafi wata girman nono. [2]
Nonuwan mace suna fara girma ne daga lokacin da ta kai mizanin balaga (puberty) wanda yake farawa daga shekara 12 zuwa sama. Nono ya ƙunshi wasu ƙananan jakunkuna dunƙulallu (lobes) kimanin 15 zuwa 20, waɗanda su ne su ke samar wa da kuma adana ruwan nono (breast milk).
Ci gaban nono
[gyara sashe | gyara masomin]Ci gaban nono yana farawa tun kafin haihuwa, lokacin da jaririn da ba a haifa ba ke fara samun kan nono da kuma farkon hanyoyin shan nono (milk ducts). A wajen ’yan mata da suka shiga balaga, ƙuruciyar nono (breast buds) na bayyana kuma su rikide zuwa naman nono (mammary tissue). Nono yana fara tashi da yin girma, sannan kuma fata mai zagaye kan nono (areola) tana yin duhu.
A tsawon rayuwa kafin mace ta shiga zaman saukar haila (menopause), nonuwa na sauyawa a kowane wata bisa tsarin haila. Wannan yana iya jawo zafi ko kumburi kafin haila, wanda ke gushewa bayan saukar jini. Ana ganin cewa girman nono da cikar ci gabansa ba su kammala sosai ba sai lokacin da mace ta ɗauki ciki kuma nononta su fara fitar da nono (madara).

Nono na iya ci gaba da samuwa a jikin maza ma, sakamakon wani yanayi da ake kira gynecomastia, inda nono ke kumbura ko girma. Haka kuma, mata masu sauya jinsi (transgender women) na iya samun ci gaban nono ta hanyar amfani da magungunan maye gurbin hormone (hormone replacement therapy – HRT).
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Breast – Definition of breast by Merriam-Webster". merriam-webster.com. Archived from the original on 6 September 2015. Retrieved 21 October 2015.
- ↑ Lafiyata: Bayanan Kiwon Lafiya a Harshen Turanci da Hausa