Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba.
Twitter logon x logoX headquarters a 2022
Twitter, a halin yanzu an sake masa tambari i zuwa X,[1] na ɗaya daga cikin manyan kafofin sada zumunta na yanar gizo wanda kamfanin Amurka X Corp. ke kula da ita, bayan Twitter, Inc. Masu amfani da Twitter za su iya yin rubutu, da saka hotuna da bidiyo a kafar. [2]Masu amfani da ita za su wallafa sako (tweet), nuna son shi, sake wallafar (ko retweet), yin sharhi, da kuma aikawa da saƙon kai tsaye ga sauran masu amfani da ita. Masu amfani suna hulɗar da Twitter ta hanyar burauza ko mahaja ta wayar hannu.
Jack Dorsey, Nuhu Glass, Biz Stone, da Evan Williams ne suka kirkiro Twitter a cikin Maris din Shekarar 2006. An Kuma kaddamar da ita a watan Yuli na wannan shekarar. Tsohon kamfanin, Twitter, Inc., ya kasance a San Francisco, California kuma yana da fiye da ofisoshin 25 a duniya.[3] A shekara ta 2012, masu amfani da twitter fiye da miliyan 100 sun samar da tweets miliyan 340 a rana, [4]
A cikin watan Oktobar shekarar 2022, hamshakin ɗan kasuwa Elon Musk ya sa yi Twitter akan dalar ƙasar Amurka biliyan 44, wanda haka ya ba shi ikon mallakarta kuma ya zama Shugaba.[5]
↑Isaac, Mike; Hirsch, Lauren (April 25, 2022). "Musk's deal for Twitter is worth about $44 billion". The New York Times. ISSN 0362-4331. Retrieved April 26, 2022.